Header Ads

ad728
  • Breaking News

    LABARIN WASANNI

    ANSU FATI NA KARA NUNA IYAWARSA A KUNGIYAR BARCELONA.. .

    Matashin dan wasa Ansu Fati, na kara nuna kwarewar sa a fagen tamaula, bayan da ya ci kwallo a karawar da kungiyarsa Barcelona ta doke Valencia da ci 5-2.
    Kungiyoyin biyu sun fafata ne ranar Asabar a wasan mako na hudu a gasar cin kofin La Liga na kasar Spaniya.
    Ansu Fati ne ya fara zura kwallo minti biyu da fara wasa, sauran wadanda suka ci wa Barca kwallayen sun hada da Frenkie de Jong da Gerard Pique da kuma Luis Suarez da ya zura biyu a wasan.
    Ita kuwa Valencia ta zare kwallo biyu da aka zura mata ta hannun Kevin Gameiro da wadda Maximiliano Gomez ya ci daf da za a tashi daga was an.
    Fati, mai shekaru 16, matashin dan wasan da aka dauko daga karamar kungiyar Barcelona, ya fara cin kwallo a watan jiya a gasar La Liga da suka yi 2-2 da Osasuna.
    Hakan ne ya sa aka fara wasan Valencia da Fati, wanda ya koma 'La Masia' a 2012, bayan da iyayensa suka koma Spaniya daga Guinea-Bissau yana da shekara shida a lokacin.

    No comments

    Post Top Ad

    ad728

    Post Bottom Ad

    ad728