Header Ads

ad728
  • Breaking News

    Mu Koyi Sana'a

    YADDA AKE HADA SABULU A SIYAR A SAMU RIBA MAI YAWA




    DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA
    MAI JINKAI,DA SALATI GA
    SHUGABAN HALITTAN ALLAH
    ANNABI MUHAMMAD (SAW) DA
    IYALANSA DA SAHABBANSA.
    DALILIN YIN WANNAN POST DIN
    Nayi wannan post dinne don
    taimakon matasanmu maza da mata
    game da abinda yashafi
    SANA'A.Nayi tattaki zuwa wajen da
    akeyin wannan aiki badan komaiba
    sai don taimakawa al'ummata.
    Da farko dolene ka tanaji
    wadannan abubuwa....
    1.Gishirin Soda
    2.Alayyadi
    3.Ruwa
    4.Kumfa
    5.Kala
    6.Stati
    7.Turare.
    Bayan katanaji wadannan
    abubuwan, kawai ka auna ruwa
    kofi hudu,sai ka auna gishirin
    sodannan kofi daya ka zuba
    aciki,sai kabarshi ya kwana daya
    idan kahadashi kamar da karfe
    goma 10:00am to sai karfe 10:00Na
    safiyar gobe yayi sannan ka cigaba
    da hadashi
    Idan ka dauko wannan ruwan daka
    hadashi da gishirin soda saika auna
    cikin kofi daya,sai ka auna alayyadi
    cikin kofi hudu sai kasa sanda ko
    muciya karinka juyawa idan kafara
    juyawa ya dame to sai kuma kazuba
    kumfa sai kaci gaba da juyawa sai
    ka zuba kala da turare da statinnan
    saika cigaba da juyawa sai ka dauko
    container ka zuba idan yasha iska
    zakasha mamaki da yardan Allah.
    Idan kajika gishirin sodan nan
    karkasa hannu dan zai konaka,Idan
    kuma Allah ya aikoma ka kone
    bakasaniba,kanajin zafi kawai sai
    kashafa man Alayyadi a wajen da
    ya kone to bazai tashiba da yardan
    Allah,Idan kuma akai sakaci aka
    sha to za'a fa mutu Allah yakare,mu
    kuma sai mu kiyaye mu kaudashi a
    inda yara bazasu ta6aba.
    DA FATAN ALLAH YASA MUDACE
    KUMA MU AMFANA DA ABINDA
    MUKA KOYA.

    No comments

    Post Top Ad

    ad728

    Post Bottom Ad

    ad728